Shirin Muhallinka Rayuwarka ya yi nazari ne akan tallafin da Manoma ke samu a Najeriya, musamman a lokacin da kasar ke kokarin karkatar da tattalin arzikinta daga dogaro da mai zuwa noma. Shirin ya ziyarci Bunkure inda a Jihar Kano inda ya tattauna da kanana da kuma manyan manoma.
Sauran kashi-kashi
-
Muhallinka Rayuwarka Yadda tsananin zafin rana ke wa jikin dan adam illa Shirin "Muhallinka Rayuwarka" ya yi dubi ne kan yadda ake fama da zafin rana a Afirka, ciki har da Arewacin Najeriya wanda yanayin kan kai sama da maki 40 na ma’aunin sa.28/05/2023 19:43
-
Muhallinka Rayuwarka Matsalar bacewar wasu nau'in itatuwa a yankunan mu A cikin shirin muhalinka rayuwar ka Nasiru Sani ya mayar da hankali a kan daya daga cikin matsaloli na bacewar iatatuwa a wasu yankuna,al'amarin da ya kai hukumomi daukar mataki na samar da shirin sake shuka irin wadanan uiatce tare da goyan bayan kungiyoyi.Nasiru Sani ya jiyo ta bakin masana da masu ruwa da tsaki dangane da wannan matsala.20/05/2023 21:30
-
Muhallinka Rayuwarka MDD- Kudin da ake kashewa wajen sayen ruwan roba ya kai ayi amfani dasu wajen samar da ruwan sha A wannan shirin na Muhallin ka Rayuwar ka, shirin dake tattauna wa da masu ruwa da tsaki kan sauyi ko dumamar yanayi da kuma uwa uba fannin noma da kiwo, wanda Nasiru Sani ke jagoranta.Shirin na wannan mako zaiyi dubi ne kan wani rahoto da Majalisar dinkin duniya ta bayana cewar kudin da ake kashewa wajen sayen ruwan roba ya kai ayi amfani dasu wajen samar da wadataccen ruwan sha a fanfunan daukacin al’uma a duniya.13/05/2023 19:39
-
Muhallinka Rayuwarka Rahoton hadin-gwiwar kungiyoyin manoman Najeriya dake gargadi kan yawan amfanin gonar da ake sacewa Shirin namu a wannan makon, zai duba rahoton hadin-gwiwar kungiyoyin manoman Najeriya dake gargadi kan yawan amfanin gonar da ake sacewa musamman a gonakin arewacin kasar a daidai wannan lokacin na girbi, satar hatsin da rahoton ke cewa zai shafi girbin bana ta fannin karanci da tsadar cimmaka.29/10/2022 19:47
-
Muhallinka Rayuwarka Yadda shaye-shaye ke taka rawa wajen gurbata muhalli Shirin Muhallinka tare da Nasiru Sani ya duba yadda ta'ammali da miyagun kwayoyi ke taka rawa sosai wajen gurbata muhalliu, kamar yadda binciken masana ya tabbatar.22/10/2022 20:02