Libya

An ceto bakin haure sama da 100 daga teku a Libya

REUTERS/Giorgos Moutafis

Masu gadin gaban teku a kasar Libya sun yi nasarar ceto wasu bakin haure akalla 120 da kwale-kwaken su ya sami matsala a tsakiyar teku yau lahadi.

Talla

Tun juma'a ne dai bain haure suka tashi daga garin Sabratha dake da nisan kilomita 70 daga birnin Tripoli, amma kuma suna cikin tafiya kwale-kwalen na su ya sami matsala.

Bayanai na nuna bakin hauren sun fito ne daga kasashe daban-daban daga nahiyar Africa.

Koda a jiya Asabar Hukumomin kasar Libya sun bayyana cewa sun kama bakin haure 400 dake neman tsallakawa turai ta teku.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI