Sudan ta Kudu

Salva Kirr ya bada umarnin harbe duk sojan da ya ci zarafin mata

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir

Shugaban Sudan Salva Kiir, ya bada umarnin cewa duk wani sojan kasar da aka kama da laifin yiwa wata mace fyade a harbe shi.

Talla

Shugaban wanda yake kokarin kwantar da hankulan ‘yan kasar bayan tarin korafe-korafe da aka gabatar na yiwa mata fyade da ake zargin sojan kasar da aikatawa.

Salva Kirr ya ce gwamnatinsa ba zata lamunci cigaba da aikata wannan ta`asa ba, dan haka ne ta dauki matakin tsattsauran hukuncin kan duk sojan da aka kama da laifin.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ne dai ya bankado aikata munanan laifukan na cin zarafin mata da ake yi a kasar, wanda hakan ya tada hankulin gwamnatin da kuma kungiyoyin dake baiwa al`ummar kasar agaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI