Isa ga babban shafi
Gambia

Gambia zata cigaba da zama a karkashin ICC - Barrow

Shugaban kasar Gambia Adama Barrow a birnin Banjul.
Shugaban kasar Gambia Adama Barrow a birnin Banjul. REUTERS/Thierry Gouegnon

Shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya sanar da dawo da kasar karkashin kotun ICC inda ya yi watsi da matakin tsohon shugaba Yahya Jammeh, da janye kasar daga kotun da ke hukunta laifukan yaki.

Talla

Barrow ya sanar da daukar matakin ne bayan tattaunawarsa da babban Jami’in da ke kula da huldar tarayyar turai da kasashen duniya Neven Mimica.

Wannan na zuwa kuma a yayin da ofishin shugaban kasar ta Gambia, ya sanar da cewa dakarun ECOWAS zasu ci gaba da aiki a kasar har tsawon watanni uku.

A baya gwamnatin tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh ta zargi kotun da nuna wariya ga kasashen nahiyar Afrika, ta yadda suke kauda kai ga da dama daga cikin laifukan da shugabannin kasashen nahiyar turai ke aikatawa, da suka cancanci a gurfanar da su a gaban kotun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.