Isa ga babban shafi
Britaniya-Afrika

Boris Johnson na ziyarar aiki a Afirka

Sakataren harkokin wajen Britaniya Boris Johnson
Sakataren harkokin wajen Britaniya Boris Johnson REUTERS/Neil Hall
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
Minti 1

Sakataren harkokin Birtaniya Boris Johnson zai fara ziyarar aikin sa na farko a nahiyar Afirka a yau talata inda zai ziyarci kasar Gambia, dan ganawa da sabon shugaban kasar Adama Barrow.

Talla

Ziyarar Johnson za ta zama ita ce ta farko da wani Sakataren harkokin wajen Birtaniya zai kai tun bayan samun yancin kan kasar daga Birtaniya a shekarar 1965.

Kasar Gambia na daya daga cikin kasashe renon Ingila da ke kungiyar Commonwealth kafin tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya janye ta.

Daga Gambia, Johnson zai ziyarci Ghana inda zai gana da shugaba Nana Akuffo-Addo.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.