Sudan

Ana bukatar dala miliyan 110 don tallafawa yara a Sudan - UNICEF

Wasu yara 'yan makaranta da yaki ya raba da gidajensu yankin Darfur
Wasu yara 'yan makaranta da yaki ya raba da gidajensu yankin Darfur dabangasudan.org by (Albert González Farran/Unamid)

Hukumar da ke kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ta bayyana kafa wani asusun neman tallafin dala miliyan 110, don taimakawa yaran da ke fama da matsalolin rashin abinci mai gina jiki a kasar Sudan.

Talla

UNICEF ta ce akalla kashi 13 cikin dari na yaran nahiyar Africa, na fama da matsalolin rashin abinci mai gina jiki.,

Hukumar ta ce yara ‘yan kasa da shekaru biyar a Duniya miliyan biyu ne ke fuskantar wannan matsala ta karancin abinci mai gina jiki a kasar Sudan.

Bugu da kari hukumar ta ce, akwai wasu yara miliyan biyu da tashe-tashen hankulan da ke faruwa a Darfur da kuma wasu yankunan kudu da arewacin Kordofan da ke gabar kogin Nil, mafi yawancin yaran an raba su da mahaifansu sakamakon rikicin.

Bayan haka wasu yara sama da miliyan uku ne da ke yankin da ake fama da tashin hankalin suka kauracewa makarantu.

Lisafi dai ya nuna cewa a cikin shekaru biyar da suka gabata, hukumar UNICEF ta kashe fiye da dalar Amurka miliyan dari biyar a kasar Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.