Isa ga babban shafi
Noma-Afirka

Tsutsar da ke yiwa amfani gona illa a kasashen Afirka

Wannan tsutsar ta haifar da asarar amfanin gona a kasashen Zambia da Zimbabwe da Afirka ta kudu da kuma Ghana
Wannan tsutsar ta haifar da asarar amfanin gona a kasashen Zambia da Zimbabwe da Afirka ta kudu da kuma Ghana (CABI (Centre for Agriculture and Biosciences International)/AFP
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
1 Minti

Majalisar Dinkin Duniya ta kira wani taron gaggawa dan tattaunawa kan yadda za a magance wata tsutsa da yanzu haka ta ke yiwa amfani gona illa a kasashen Afirka da dama.

Talla

David Phiri, Babban jami’in Hukumar Samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce wannan shi ne karo na farko da aka samu tsutar irin wanda ake ganin an Yankunan kasashen Amurka.

Tuni wannan tsutsa ta haifar da asarar amfanin gona a kasashen Zambia da Zimbabwe da Afirka ta kudu da kuma Ghana, yayin da aka samu labarin ta kuma isa kasahsen Malawi da Mozambique da Namibia.

Ana saran masana daga kasashe 13 za su kwashe kwanaki uku suna tattaunawa a Harare dan samo hanyar magance matsalar.

Cibiyar kula da kimiyar gona ta bayyana fargabar cewar, tsutsar na iya haifar da karancin abinci a duniya, ganin yadda ta ke yaduwa cikin sauri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.