Isa ga babban shafi
Najeriya

An kai hare hare a Tashar Gamboru a Maiduguri

Sojoji sun bude hanyar zuwa Baga daga Maiduguri
Sojoji sun bude hanyar zuwa Baga daga Maiduguri RFI Hausa/Bilyaminu
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
1 min

Wasu ‘Yan kunar bakin wake 6 sun kai hare hare a bakin wata tashar mota da ake kira Muna Garej a cikin garin Maiduguri kan hanyar zuwa garin Gamboru Ngala da ke Jihar Borno.

Talla

An kai harin ne a tashar da ake lodin zuwa Gamboru da ke kan iyaka da kasar Chadi.

Wakilin RFI Hausa a Maiduguri Biyaminu Yusuf ya ce mace ce ta fara tayar da bom din da ke jikinta a bakin tashar da motoci ke lodin zuwa Gamboru.

Sannan ya ce harin ya jikkata ‘yan kato da gora 8 wadanda yanzu haka suke karban Magani a asibiti.

Wannan na zuwa a yayin da rundunar sojin Najeriya ta bayyana yin nasarar murkushe wani yunkurin mayakan kungiyar Boko haram na kutsa kai cikin birnin Maiduguri

Mutanen garin sun ce tun jiya suke jin karar harbe harbe.

Bayani sun tabbatar da cewar sojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka mayakan da dama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.