Nijar

Gwamnatin Nijar ta kawo karin haske kan kudin Cfa milliyan dubu 200 daga Areva

Hassoumi Massaoudou Ministan kudin Nijar
Hassoumi Massaoudou Ministan kudin Nijar

Gwamnatin Nijar ta musanta bayanan da wata jarida mai zaman kanta da ake bugawa a kasar ta wallafa da ke zargin cewa an boye kudaden kasar cfa milyan dubu 200 a wani asusu da ke Dubai.

Talla

A cewar jaridar Le Courrier, lamarin ya faru ne tun a shekara ta 2011, kuma bisa ga dukkan alamu kudaden an same su ne daga cinikin Uranium.

To sai dai Hassoumi Massaoudou daraktan ayyukan mulkin fadar shugaban kasar a wancan lokaci sannan kuma ministan kudi a yanzu, ya ce ba haka zance yake ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI