Sudan ta Kudu

Manyan jami'an gwamnatin Sudan ta Kudu na yin murabus

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir The Japan Times

Wasu manyan jami’an Sudan ta Kudu biyu sun janye daga kotun sojin kasar bisa zargin gwamnatin kasar na yiwa kotun katsalandan cikin alamurran tafiyar da harkokinta, inda har ta kai ba za a iya hukuntar da sojojin da suka aikata laifufuka ba.

Talla

Birgediya Janar Henry Oyay Nyago da kuma Kanar Khalid Ono Loki, sun yi marabus ne kwanaki kadan bayan da wani janar na soji da kuma ministan kwadagon kasar suka sauka daga mukamansu.

Tun daga shekara ta 2013 Sudan ta Kudu mai arzikin man fetur, ta afka cikin yakin basasa, bayanda shugaban kasar salva Kiir dan kabilar Dinka, ya kori mataimakinsa Riek Machar dan kabilar Nuer.

Tun daga lokacin ne kazamin fada ya barke tsakanin masu biyayya ga bangarorin biyu, wanda ya rikide zuwa fadan kabilanci, wanda ta kai sai da Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin aukuwar kisan kare dangi a kasar makamancin wanda ya faru a Rwanda.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI