Najeriya-Afrika ta kudu

Majalisar Najeriya ta Soki hare-hare kan ‘yan kasar a Afrika ta Kudu

Masu gangamin adawar kyamar baki a Afrika ta Kudu
Masu gangamin adawar kyamar baki a Afrika ta Kudu REUTERS/Mike Hutchings

Majalisar wakilan Najeriya ta amince da wani kuduri da ke yin kakkausar suka dangane da hare-haren da ake ka iwa Najeriya da ke zaune a Afirka ta Kudu.

Talla

Hakazalika kudurin ya bukaci gwamnatin Muhamadu Buhari da ta kira jakadan kasar da ke Pretoria zuwa gida, sakamakon kaddamar da hare-haren wariyar jinsi a kan ‘yan Najeriya tun a ranar juma’ar da ta gabata.

Ko a shekarar da ta gabata ‘yan Najeriya sun fuskanci irin wannan matsala tare da kashe akalla mutane 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.