Afrika ta kudu

Gwamnatin Africa ta Kudu na lallashin jama'a da su daina kyamar baki

Shugaban Africa ta Kudu Jacob Zuma
Shugaban Africa ta Kudu Jacob Zuma REUTERS/Mike Hutchings

Gwamnatin kasar Africa ta kudu ta bukaci mutan kasar da su kwantar da hankula sakamakon kazamin boren kyamar baki da ake yi a wasu sassan kasar da ya kai ga kona shaguna da gidajen jama’a masu yawa.

Talla

A dan tsakanin nan an sha samun rahotannin barnata kaddarorin baki sakamakon rashin ayyukan yi a fadin kasar.

A makon jiya sama da shaguna 20 aka barnata a yankin Atteridgeville a bayan garin Pretoria, yayin da gidajen baki 12 aka kaiwa hari a Rosettenville dake kudancin Johannesburg.

Ministan Harkokin cikin gida na kasar Africa ta Kudu Malusi Gigaba ya fadawa taron manema labarai cewa jama’a su dai kaiwa baki hare-hare.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.