Isa ga babban shafi
Libya

An haramtawa baki yawo a Gabashin kasar Libya

Wasu bakin haure da masu gadin gaban ruwan Libya suka kama kwanan baya.
Wasu bakin haure da masu gadin gaban ruwan Libya suka kama kwanan baya. Reuters/路透社
Zubin rubutu: Garba Aliyu
Minti 1

Hukumomi a gabashin kasar Libya sun kafa dokar hana baki zirga-zirga a yankin musamman masu shekaru tsakanin 18 zuwa 45, inda ake bukatar dole sai an nemi rakiyar jami'an tsaro.

Talla

Janar Abdelrazak al-Nadhouri, Babban Kwamandan Dakarun Gwamnatin mai kulada yankin Gabashin kasar ya fadi cewa dole ne sai an karbi izinin zirga-zirga a yankin saboda matakan tsaro.

Ya ce akwai matsalar tsaro dake bukatar daukan wannan mataki.

Kazalika an haramtawa mata masu shekaru kasa da 60 fita kasar ba tare da wani jagora ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.