Somalia

Fari zai shafi mutane sama da miliyan 3 a Somalia

Fari zai shafi mutane sama da miliyan 3 a Somalia
Fari zai shafi mutane sama da miliyan 3 a Somalia

Sabon shugaban Somalia Mohammed Abdullahi Farmajo ya sanar cewa kasarsa na cikin bala'i na fari mai tsanani wanda ya shafi mutane sama da miliyan uku.

Talla

Tuni Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kasashen Afrika uku da suka kunshi Najeriya da Sudan ta Kudu da Somalia da za su fuskanci yunwa a bana

Shugaban na Somlia ya nemi taimakon kasashen duniya su gaggauta kawo dauki domin kaucewa abin da zai biyo baya daga matsalar da farin ya haifar.

Tuni dai Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin cewa Somalia zata fuskanci yunwa a karo na uku cikin shekaru 25 bayan matsalar da aka fuskanta a 2011 inda aka samu mutuwar mutane dubu 260.

Hukumar ta ce kusan mutane miliyan 6 da rabi ke bukatar taimakon gaggawa a Somalia ciki kuma har da miliyan uku da matsalar yunwar ta fi kamari.

Alkalumman Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO sun bayyana cewa yara kusan dubu 400 ke fama da rashin abinci mai gina jiki

Baya ga yunwa, farin kuma ya haifar da cututuka da suka hada da zawo da amai da kyanda ga miliyoyan ‘yan kasar

Tuni dai aka kaddamar da dokar ta baci akan Sudan ta Kudu da ita ma ke fama da yunwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.