Masar

Babbar Kotun Masar ta wanke Hosni Mubarak

Tsohon Shugaban Masar Hosni Mubarak
Tsohon Shugaban Masar Hosni Mubarak REUTERS/Stringer/Files

Babbar kotun daukaka kara a Masar ta wanke tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak ga tuhumar laifin kisan da aka yi wa wasu masu zanga-zanga a lokacin da aka kifar da gwamnatinsa a shekara 2011, abin da ya kawo karshen jagorancinsa na tsawon shekaru 30.

Talla

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake yi masa shari’a ta karshe a yau Alhamis game da zargin. Kuma hukuncin kotun daukaka karar shi ne na karshe a tsarin dokar Masar.

A farko dai an yanke wa Murabak mai shekaru 88 da haihuwa hukuncin daurin rai da rai a shekara ta 2012 sakamakon zarginsa da hannu wajen kashe mutane 850 da ke zanga-zangar kyamar gwamnatin shi.

An tuhumi tsohon shugaban ne da ba jami’an tsaro umurnin kisan masu zanga-zangar kafin ya yi murabus a 2011.

Akwai dai mambobin gwamnatin Mubarak da dama da kotu ta wanke yayin da wanda ya gaje shi Mohammed Morsi da magoya bayan jam’iyyarsa ta ‘yan uwa Musulmi ke fuskantar hukuncin kisa da daurin rai da rai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI