Najeriya

Buhari ya zanta da Sarkin Morocco a tarho

Sarki Mohammed na Morocco Ya kai ziyara Sudan ta Kudu
Sarki Mohammed na Morocco Ya kai ziyara Sudan ta Kudu REUTERS

Sarki Mohammed na shida na Morocco ya tattauna da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta tarho a London inda da ake diba lafiyarsa. Kakakin shugaban na Najeriya Femi Adeshina ya fadi a cikin sanarwar da ya fitar a yau Alhamis cewa Sarkin Morocco ne ya bukaci yin tattaunawar da Buhari.

Talla

Sanarwar ta ce Sarkin na Morocco ya tambayi lafiyar Buhari tare da bayyana gamsuwarsa.

Shugabannin sun kuma tattauna akan halin da ake ciki ga aikin shinfida bututun da zai ratsa Morocco zuwa kasashen Turai daga Najeriya.

Sannan Sarkin ya sanar da Buhari game da bukatar Morocco na shiga kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS tare da mika godiya ga goyon bayan da suka samu na dawo da kasar a Kungiyar Tarayyar Afrika.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.