Kungiyoyin ta’adda uku a Sahel sun hada kai
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Manyan kungiyoyin ta’adda guda uku da ke barazana a yankin Sahel sun sanar da hadewa a matsayin kungiya guda da za ta kunshi dukkanin mayakansu. Kungiyoyin sun sanar da hadewa ne a cikin wani sakon bidiyo da suka aika wa Kamfanin dillacin labaran Mauritania ANI.
Kungiyoyin uku sun kunshi kungiyoyin ta’ adda biyu a Mali Ansar Dine da ‘yan tawayen Macina Brigades da kuma kungiyar Al Murabitoun ta Algeria, dukkaninsu da ke da alaka da Al Qaeda.
Kungiyoyin sun amince da kafa sabon suna a matsayin kungiyar da ke taimako addinin Islama da musulmi karkashin jagorancin Iyag Ag Ghaly shigaban Ansar Dine ta Mali.
A cikin sakon bidiyon, shugaban kungiyoyin Ag Ghaly ya kara jaddada mubaya’arsu ga shugaban Al Qaeda Ayman al Zawahiri.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu