Najeriya

Manoma a Filato na kuka da ayyukan hako Ma’adinai

A Jihar Filato aka fi yin noman Dankalin Turawa
A Jihar Filato aka fi yin noman Dankalin Turawa RFI Hausa/Awwal

A yayin da gwamnatin tarayyar Najeriya ke fadi-tashi domin ganin ta habaka aikin gona domin samar da wadataccen abinci a cikin kasar maimakon dogaro da shigowa da shi daga ketare, amma manoma a wasu yankuna na nuna damuwa dangane da yadda ayyukan hako madinai ke haddasa illoli ga aikin gona. A jihar Filato daya daga cikin yankunan da aka share tsawon shekaru ana hako ma’adinin kuza, an bayyana cewa wannan aiki na kawo cikas matuka ga manoma kamar yadda wakilin RFI Hausa a Jos Muhammad Tasiu Zakari ya aiko da rahoto.

Talla

Manoma a Filato na kuka da ayyukan hako Ma’adinai

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.