Gambia

Gambia ta kulla sabuwar dangantaka da Senegal

Shugaban kasar Senegal Macky Sall tare da shugaban kasar gambia Adama Barrow tare da iyalansu
Shugaban kasar Senegal Macky Sall tare da shugaban kasar gambia Adama Barrow tare da iyalansu SEYLLOU / AFP

Gwamnatocin kasashen Gambia da Senegal sun sanar da sake kulla alaka mai karfi, ta fanonin tattalin arziki da tsaro.

Talla

Shugabam Gambia Adama Barrow ya sanar da cimma wannan kawace yayin kammala ziyarar kwanaki 3 da ya kai Senegal, inda ya ce duk bayan watanni shida kkusoshin kasashen biyu zasu rika taron tattaunawa kan cigaban da ake samu.

Karo na farko kenan da kasashen biyu suke cima yarjejeniyar bayan saukar tsohon shugaban kasar ta Gambia Yahya Jammeh, wanda gwamnatinsa ke da tangardar diflomasiya da Senegal.

Barrow y ace wannan dam ace ga Gambia da ke kokarin sake fasalta rundunar sojinta, domin igaba da gudanar da ayyukan tsaro da atasaye tare da sojin Senegal da ke cigaba sda zama a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI