Liberia

Wata mace da ta warke cutar Ebola shekaru uku da suka gabata ta mutu a kasar Liberia

Fasalin abinda ke sa cutar ebola
Fasalin abinda ke sa cutar ebola CDC/Frederick A. Murphy

A kasar Liberia wata mace wadda ta sha da kyar bayan da ta kamu da cutar Ebola shekaru uku da suka gabata ta mutu, yanzu haka sakamakon tangarda wajen haihuwa. 

Talla

A watan Nuwamba na shekara ta 2014 ne dai Uwargida Salome Karwah aka sanar da cewa ta warware daga cutar Ebola har kafofin yada labarai suka yi ta tallata ta.

Rahotanni na cewa ta mutu ne wajen haihuwa na danta na hudu.

Mijinta ya ce bai fidda tsammanin guggubin cutar Ebola ne ya kashe ta ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI