Kwamitin Majalisar Malamai ta jihar Kano da ke Arewacin Najeriya na ci gaba da bitar daftarin dokar aure da mai Martaba Sarki Sunusi na biyu ya gabatar da nufin magance matsalolin da ke haddasa mutuwar aure. Ana sa ran nan da kwanaki 10 kwamitin zai kammala nazarinsa kafin daga bisani a kaddamar da kundin dokar ga majalisar jihar. A zantawarsa da Abdurrahman Gambo Ahmad, daya daga cikin malaman kwamitin, Sheik Abdullahi Uwais ya ce, akwai gyara a doka.
Sauran kashi-kashi
-
Bakonmu a Yau Sabuwar gwamnatin Katsina ta sha alwashin magance matsalar tsaro Sabuwar gwamnatin jihar Katsina ta Najeriya da ta yi rantsuwar kama-aiki a wannan Litinin ta bayyana sabbin matakan da za ta dauka wajen magance matsalar tsaro, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare durkusar da tattalin arzikinta.29/05/2023 03:22
-
Bakonmu a Yau Farfesa Usman Muhammad kan bikin rantsar da sabon shugaban Najeriya A ranar 29 ga watan Mayun 2023, aka rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin sabon shugaban Najeriya domin maye gurbin tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari, wanda ya kawo karshen wa’adin mulkinsa na shekaru 8.29/05/2023 03:38
-
Bakonmu a Yau Zainab Ahmed kan basussukan da ake bin Najeriya Yayin da gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke kawo karshen wa’adin ta a ranar litinin mai zuwa, daya daga cikin zargin da ake mata shine na ciwo basussuka daga hukumomin duniya, wadanda suka yiwa kasar dabaibayi.26/05/2023 03:45
-
Bakonmu a Yau Kungiyar tarayyar Afrika ta cika shekaru 60 ga kafuwa kungiyar tarayyar Afrika ta cika shekaru 60 da kafuwa a dai dai wannan lokaci da nahiyar ke fuskantar matsaloli da kalubale kala kala musaman ma na tsaro fadace fadace tsakanin dakarun gwamnati da kungiyoyin yan tawaye, ko kuma da kungiyoyin dake ikrarin jihadi, da kuma na yan bindiga.To domin jin irin nasarorin da aka samu a cikin wadannan shekaru, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abbati Bako masanin siyasar duniya a jami'ar Bayaro dake Kano Najeriya.25/05/2023 03:42
-
Bakonmu a Yau Birtaniya na shirin takaita baiwa dalibai yan kasshen ketare Biza Gwamnatin Birtaniya ta takaita adadin takardun bizar da take bai wa dalibai ‘yan kasashen waje da ke karatu a kasar, biyo bayan hauhawar adadin bakin da ke shiga cikin Birtaniyar da sunan iyali ko ‘yan uwan daliban.24/05/2023 03:35