Bakonmu a Yau

Tsohon shugaban SEMA a Borno Grema Terab

Sauti 03:29
'Yan gudun hijirar rikicin Boko Haram na kukan yunwa a Borno
'Yan gudun hijirar rikicin Boko Haram na kukan yunwa a Borno RFIHAUSA/Awwal

A daidai lokacin da tawagar Majalisar Dinkin Duniya ke gudanar da ziyarar gani da ido kan halin da rikicin Boko Haram ya jefa mutanen yankin tafkin Chadi, ‘Yan gudun hijira da dama ne mafi yawancinsu mata suka gudanar da zanga-zangar neman kyautata rayuwarsu a cikin sansanoninsu da ke Maiduguri a jihar Borno. ‘Yan gudun hijirar na kukan yadda ake karkatar da kudi da kuma kayayyakin agajin da ya kamata ace sun zo a hannunsu. Awwal Janyau ya tattauna da Grema Terab tsohon shugaban hukumar agajin gaggawa ta SEMA a jihar Borno.