Najeriya

Ana bikin ranar mata ta duniya

Ana ba iyaye mata da 'yan uwa Faranni a ranar Mata ta duniya.
Ana ba iyaye mata da 'yan uwa Faranni a ranar Mata ta duniya. REUTERS/Sergei Karpukhin

A yau 8 ga Maris Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar mata ta duniya, inda ake amfani da ranar wajen nazari kan matsalolin da mata ke fuskanta da niyyar janyo hankalin wadanda ke da ikon kawo sauyi.

Talla

Tun a farkon karni na 19 ake gudanar da bikin ranar Mata a duniya. Bikin ranar kuma ya shafi nazari akan hakkokan Mata da samun daidaito tsakaninsu da Maza.

Daya daga cikin bukatun matan shi ne ganin sun yi kafada da maza wajen samun madafan iko a karkashin mulkin dimokiradiya.

amma ga alama a kasahse masu tasowa har yanzu akwai sauran rina a kaba.

Farfesa Hauwa Biu ta Jami’ar Maiduguri na ganin har yanzu an bar mata a baya kasashe masu tasowa inda ta ce ana amfani da mata ne kawai a lokacin Kamfen amma da an ci zabe an manta da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.