Bakonmu a Yau

Dakta Isa Abdullahi masanin tattalin arziki a Najeriya

Wallafawa ranar:

‘Yan Najeriya sun fara mayar da martani ga matakin hukumar kwastam na kwace duk wata mota da aka shiga da ita kasar da ba a biya ma ta harajin gwamnati ba, ko kuma tana dauke da takardu na bogi. ‘Yan kasar na kallon umurnin a matsayin gazawar hukumar na kasa karbar kudaden akan iyakoki, da kuma zargin cin hancin da ake yi wa jami’anta da ke taimakawa masu shigar da motocin ta bayan fage. Majalisar Dattawa dai ta yi watsi da matakin. Dangane da wannan ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dakta Isa Abdullahi na sashen nazarin tattalin arziki a Jami’ar Kashere Jihar Gombe.  

Shugaban Hukumar Kwastam na Najeriya Kanal Hamid Ali mai ritaya
Shugaban Hukumar Kwastam na Najeriya Kanal Hamid Ali mai ritaya custom