Najeriya

Stephanie Linus ta zama jakadiyar MDD a Afrika

Shahararriyar jarumar fina-finan Nollywood a Najeriya, Stephanie Linus
Shahararriyar jarumar fina-finan Nollywood a Najeriya, Stephanie Linus guardian.ng

A yayin da ake bikin ranar mata ta duniya, Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da fitacciyar Jarumar fina-finan Nollywood, Stepahie Linus a matsayin jakadiyarta da za rika taimaka ma ta wajen kare lafiyar mata a Yammaci da kuma Tsakiyar Afrika.

Talla

Hukumar Kula da ci gaban al’umma ta Majalisar Dinkin Diniya ta ce, Linus za ta taka rawar gani ta hanyar wayar da kawunan al’umma game da matsalar mace-macen mata masu juna-biyu da kuma kawo karshen aurar da kananan yara a Afrika.

Kori Muhammad Habeeb, babbar jami’a a hukumar Kula da Iyalai ta Majalisar Dinkin Duniya ta shaida wa RFI hausa cewa, Mrs. Linus za ta rika ganawa da sarakun gargajiya da jami’an gwamnatin don shawo kan matsalar mutuwar mata wurin hahuwa.

Kori Muhammad Habeeb ta koka game da wannan matsala ta mace-macen mata masu juna biyu, in da ta ce, matsalar ta tsananta a kasashen Afrika da suka hada da Najeriya.

A lokacin da ta ke gabatar da jawabi jim kadan da kaddamar da ita a wani gagarumin biki da aka gudanar a birnin Legas na Najeriya a yau Laraba, Mrs. Stephanie Linus ta ce, babbar girmamawa ce a gare ta da aka zabe ta a matsayin jakadiyar hukumar kula da ci gaban al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya don kare lafiyar mata a kasashen Afrika.

Sabuwar Jakadiyar ta koka kan yadda dubban mata ke rasa rayuakansu a Afrika saboda matsalolin da ke da nasaba da juna-biyu. Sannan ta ce, kowacce mace na da hakkin samun kulawa da lafiyarta .

A cewar Linus, babban burinta shi ne tabbatar da haihuwa cikin sauki da kuma samun makoma ta gari ga kananan yara. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.