Africa ta Kudu

Africa ta Kudu ta janye kudurinta na ficewa daga kotun ICC

Babbar mai gabatar da kara ta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC Fatou-Bensouda.
Babbar mai gabatar da kara ta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC Fatou-Bensouda. UN Photo/Eskinder Debebe

Kasar Afrika ta Kudu ta janye kudurinta na ficewa daga karkashin kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, bayanda babbar kotun kasar ta yanke hukuncin cewa ficewarta daga ICC, ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Talla

Tun a wata Oktoban shekarar da ta gabata ne Africa ta Kudu ta bayyana aniyarta ta ficewa daga kotun ta ICC.

To sai dai tun a waccan lokacin babbar jam'iyyar adawa a kasar, ta Democratic Alliance ta ruga kotu, don neman dakatar da kudurin, inda ta yi muhawarar cewa dole gwamnatin kasar ta nemi sahalewar majalisa kafin yanke hukunci.

Kasashen Africa da suka hadar da Burundi, Namibia da Africa ta Kudun ne suka bayyana aniyar ficewa daga karkashin kotun ta ICC, bisa zargin kotun da suke na nuna banbanci wajen gurfanar da masu manyan laifuka tsakanin nahiyar Africa da Turai.

Shirin ficewar ya haifar da mahawara zafi a fadin kasar, kafin soke matakin da kasar tayi a wasikar da ta rubutawa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI