Somalia

Iyaye a Somalia na zabar yaron da zasu bai wa abinci saboda yunwa

Wata uwa da 'ya'yanta a sansanin 'yan gudun hijira na Al-cadaala da ke birnin Mogadishu na Somalia.
Wata uwa da 'ya'yanta a sansanin 'yan gudun hijira na Al-cadaala da ke birnin Mogadishu na Somalia. REUTERS/Feisal Omar

Rahotanni Daga sassan kasar Somalia dake fama da yunwa sun nuna cewa matsalar tayi kamarin da a halin yanzu, iyaye zaben yaran da zasu bai wa abinda zasu ci su ke yi, saboda rashin abincin.

Talla

Fatuma Abdille, wata uwa da ta tsallake rijiya da baya, wajen isa birnin Mogadshu da yaran ta 7, tace dan abinda suka samu, su kan duba yaron da yafi bukatar abincin su bashi, sauran kuma su hakura.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, da ya kai ziyarar bazata kasar, ya roki kasashen duniya da su yiwa Allah, su taimakawa kasar dan kaucewa irin bala’in da aka gani a shekarar 2011 lokacin da yunwa ta kashe mutane 260,000 a kasar.

Kungiyoyin bada agaji sun mika kokon bara ga kasashen duniya don tara dala miliyan 825 don taimakawa ‘yan Somalia akalla miliyan 6 da dubu 200, kimanin rabin al’ummar kasar.

Wata matsala da ke ciwa kungiyoyin bada agaji tuwo a kwarya kuma shi ne yadda rashin tsaro ya hana su isa ga sassan kasar da dama domin isar da kayayyakin abinci da magunguna ga jama’a.

Zalika karancin ruwan sha, ya tilastawa iyalai da dama shan ruwa marar tsafta, sakamakon haka mutane 8,000 suka kamu da cutar kwalara a kasar ta Somalia, yayinda wasu 180 suka rasa rayukansu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.