Wasanni

El Kanemi Warriors ta Maiduguri

Sauti 10:18
Tawagar kungiyar El Kanemi Warriors FC a Maiduguri
Tawagar kungiyar El Kanemi Warriors FC a Maiduguri RFIHAUSA/Awwal

Shirin Duniyar wasannin ya kai wa Kungiyar El Kanemi Warriors ziyara ne a birnin Maiduguri Jihar Bornon Najeriya, musamman kan dawowarta gida tana buga wasanninta na gasar Premier bayan samun kwanciyar hankali daga barazanar Boko Haram. Shirin ya tattauna da shugabannin kungiyar da kuma magoya bayanta.

Talla

An shafe tsawon shekaru uku saboda matsalar tsaro a Borno El Kanemi Warriors na buga wasanninta na gida a filayen Sani Abacha a Kano da kuma filin Muhammadu Dikko na Katsina jihohin yankin arewa maso yammacin Najeriya, amma yanzu kungiyar ta dawo tana buga wasanninta a filinta na El Kanemi a Maiduguri.

A shekarar 1986 ne aka kafa kungiyar El Kanemi a jihar Borno, zamanin mulkin gwamnan Jihar na soja Kanal Abdulmumuni Aminu. Kuma El Kanemi ta yi tashe a Najeriya a lokacin.

Kodayake dai El Kanemi ta fuskanci kalubale a wajajen 2007 inda ta koma buga wasa a Lig mataki na biyu a Najeriya, kafin ta sake haurowa buga Firimiya a 2012.

Rikicin Boko Haram da ya tursasawa El Kanemi buga wasanninta na gida a waje Amma hakan bai sa ta fice gasar Firimiya ba.

Magoya bayan kungiyar sun bayyana farin cikinsu da suka dawo buga wasanninsu a gida Maiduguri.

A bana El Kanemi ta buga wasanni 18 gidanta a Firimiya ba a sha ta ba, bayan ta doke Narasawa United ci 2-0. Amma Akwa United a gidanta ta samu sa’ar El Kanemi Warriors ci 1-0 mai ban haushi a wasannin mako na 11 da aka buga.

Mutanen Maiduguri dai na cika makil Idan El Kanemi na wasa, kuma a cewar kocin kungiyar Isa Ladan Bosso wannan na karawa ‘yan wasan kwazo tare da razana a bokan hamayya.

A yanzu dai El Kanemi na matsayi na biyu ne a teburin Firimiya da maki 21, tazarar maki guda tsakaninta da Plateau United.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.