Najeriya

Hannayen jarin Najeriya sun tashi bayan isowar Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa Yemi Osinbajo bayan isarsa Abuja
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa Yemi Osinbajo bayan isarsa Abuja REUTERS

Farashin hannayen jarin Najeriya sun tashi a yau Juma’a a daidai lokacin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya dawo gida bayan share sama da kwanaki 50 yana jinya a London.

Talla

An dai bude babbar kasuwar hannayen jarin kasar da ke Lagos ne jim kadan bayan dawowar shugaba Buhari a Najeriya. Kuma da misalin karfe 10 :30 na safe agogon kasar kasuwar ta samu dagawa sama da kashi daya cikin dari, farashi mafi girma da kasuwar ta samu a cikin kwanaki 30.

‘Yan kasuwar dai na da kyakkyawar fata akan kasuwar hannayen jarin bayan dawowar Buhari.

Yanzu haka kuma asusun kudaden ajiyar Najeriya da ke waje ya kai wani matsayin mafi daukaka da ba a taba ganin irinsa ba tun watan Oktoban 2015.

A yanzu dai Najeriya ta mallaki dala milyan dubu 30 a asusun, abin da ke nufin cewa an samu karin kudaden da yawansu ya kai kashi 15 cikin dari a cikin shekara daya.

Sai dai har yanzu da sauran aiki kafin cimma adadin kudin da ke cikin asusu, wanda karon farko a cikin shekara ta 2008 kudaden da ke cikinsa suka kai dala milyan dubu 64.

Najeriya dai na fuskantar matsalar tattalin arziki sakamakon faduwar farashin danyen mai da kuma fashe fashen bututun mai da tsagerun Neja Delta a kudancin kasar ka yi, matakin da ya janyo faduwar dajarar Naira.

Ayyukan tsagerun Neja Delta ya rage yawan man da Najeriya ke fitarwa a kasuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.