Na ji Sauki, Ma su mugun nufi Allah ya shirye su- Inji Buhari
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari ya ce zai koma bakin aikinsa makon gobe bayan ya dawo kasar yau Juma’a daga birnin London, inda ya shafe tsawon kwanaki 51 yana hutun jinya.
Shugaban Buhari ya samu kyakkyawar tarba a lokacin da ya ke sauka a filin jirgin Kaduna da safiyar yau Juma'a.
Bayan ya isa Abuja, Buhari ya godewa Jama’ar Najeriya dangane da Addu'o'in da suka yi masa na samun lafiya, inda ya kara tabbatar da ci gaba da gudanar da mulkinsa bisa gaskiya da amana.
"Ina shaidawa Jama'a cewa gani a gida na ji sauki, Alhamdulillahi", a cewar Buhari.
Wakilinmu daga fadar shugaban kasar a Abuja Kabiru Yusuf ya ce Buhari ya tabbatar da cewa zai koma bakin aiki sabanin wasu rahotannin da ke cewa mataimakinsa Farfesa Yemi Osibanjo zai ci gaba da mulki har ya murmure.
Na ji Sauki, Ma su mugun nufi Allah ya shirye su- Inji Buhari
Kakakinsa Femi Adeshina ya tabbatar da a Twitter cewa Buhari zai sanar da Majalisa dawowarsa kamar yadda tsarin doka ya tanadar domin ci gaba da aikinsa na shugaban kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu