Najeriya

Najeriya za ta magance rikicin Guinea Bissau

Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo
Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo REUTERS

Gwamnatin Najeriya ta ce a shirye ta ke ta taimaka wa kasar Guinea Bissau magance rikicin siyasar da ya dabaibaye ta.

Talla

Mukaddashin shugaban Najeriya, Yemi Osibanjo ya bayyana haka yayin da ya karbi Firaministan kasar Oumarou Sissco Embalo a jihar Kaduna.

Osibanjo ya ce, Najeriya za ta ci gaba da sanya hannu a shirin kungiyar  kasashen Yammacin Afrika ECOWAS na ganin an shawo kan matsalolin da suka addabi kasar.

Firaministan ya ce ya ziyarci Najeriya ne don ci gaba da tuntuba kan halin da kasar su ke ciki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.