An soma shari’ar ‘Yan Boko Haram a Nijar
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A Jamhuriyar Nijar an fara shari’ar sama da mutane dubu daya da ake zargi da yin alaka da kungiyar Boko Haram, mutanen da aka kama mafi yawansu a jihar Diffa sannann ake tsare da su a sassa daban daban na kasar.
Ana dai gudanar da wannan shari’a ne a asirce kuma a cikin tsauraran matakan tsaro.
Mai shigar da kara na gwamnatin Jamhuriyar Nijar Chaibou Samna, ya ce an fara shari’ar ne tun a ranar 2 ga wannan watan Maris, kuma wadanda ake tuhumar sun fito ne daga kasashen Mali da Nigeria da kuma ‘yan Nijar.
Ana zargin mutanen ne da aikata laifufuka daban daban masu alaka da ta’addanci, kuma za a share tsawon watanni da dama kafin a kammala Shari’ar.
Tuni dai kotun ta fara zartar wa wasu daga cikinsu hukuncin dauri da ya kama daga shekaru uku zuwa tara a gidan yari.
Domin tabbatar da an yi wadanda ake zargin adalci, kotun ta aike da kwararrun alkalai domin tattaro bayanai daga jihar Diffa inda ake zargin mutanen da aikata laifufuka, yayin da aka samar da wadanda za su rika yi wa mutanen da ake zargin fassara a gaban kotu.
Nijar dai na daga cikin kasashen yankin Tafkin Chadi hudu da kungiyar ta Boko Haram ta aikata mummar ta’asa a cikinsu, da suka hada da kisa, yin garkuwa da mutane da kuma kawo cikas ga bangaren noma da kuma tattalin arzikinsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu