Haiti

An binne tsohon Shugaban kasar Haiti

Tsohon Shugaban kasar Haiti Rene Preval
Tsohon Shugaban kasar Haiti Rene Preval REUTERS/Lucas Jackson

A jiya asabar ne aka binne tsohon Shugaban kasar Haiti Rene Preval da ya rasu ranar 3 ga watan Maris ya na mai shekaru 74. 

Talla

Hafsoshin Soji ne suka dauki akwatin gawar Rene Preval inda daruruwan mutanen kauyen suka yi masa bankwana.
Akwai abokan siyasa da suka yi fafutika tare da suka halarci bikin Jana’izar shi a Port au Prince,
Yan kasar na kalon mammacin a matsayin mutumen da ya taka gaggarumar rawa wajen tafiyar da mulkinsa kama daga shekara ta 1996 zuwa 2001 tenuwar farko ,kana kama daga shekarar ta 2006 zuwa 2011 tenuwa ta biyu a karkashin mulkin demokkradiya bisa gaskiya da adalci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.