Jamhuriyar Nijar

Sauye-sauye ta bangaren ilimi a Nijar

Dalibai a dakin  karatu
Dalibai a dakin karatu Anthony Asael/Getty

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun sanar da shirin su na kawo gyara ta fuskar koyarwa ,Ministan ilimin kasar Daouda Marthe ya bayyana haka wanda kusan mallamai na kananan makarantu 61000 za su amfana da shirin da zai taimakawa hukumomin kasar domin tanttance hanyoyin magance wasu daga cikin matsallolin dake hana ruwa gudu a wannan sashe. 

Talla

Bazoum Mohamed Ministan cikin gidan Jamhuriyar Nijar a na shi wajen ya bayyana ta yada Gwamnatin kasar ke ta kokarin shafe hawayen mallaman makaranta.
Wasu daga cikin bicinke da Gwamnatin ta yi ya sa hukumomin sun gano mallaman bogi dauke da takardun jabu,wanda hakan na daya daga cikin matsallolin da ya dace gwamnatin ta maida hankali a cewar Daouda Marthe Ministan ilimin Jamhuriyar Nijar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI