Zabtarewar bola ta yi ajalin mutane kusan 50 a Addis Ababa
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Akalla mutane kusan 50 suka kwanta dama, da dama kuma suka jikkata sakamakon zabtarewar bola da ta auku a inda ake zub da shara a wajen birnin Addis Ababa na Habasha.
Kamfanin dilancin labaran faransa AFP ya rawaito cewa akasarin wadanda abin ya shafa marasa galihune da ke rayuwa a kusa da inda ake zub da shara.
Jami’in sadarwar Yankin, Dagmawit Moges yace mata 32 da maza 14 suka mutu a hadarin, kuma akasarin su wadanda suke tone sharar ce suna neman abinda zasu sayar su sa a bakin salati.
Yankin Koshe inda lamarin ya auku, ya kasance baban juji a Addis Ababa sama da shekaru 40, kuma akwai mutane kusan miliyan 4 da ke rayuwa a yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu