Faransa-Najeriya

''Faransa ba zata goyi bayan kafa kasar Biafra ba''

Kasar Faransa ta ce ba zata goyi bayan duk wani yunkuri na masu fafutukar kafa kasar Biafra daga Najeriya ba, saboda babu dalilin yin haka.

Shugaban kasar Faransa François Hollande
Shugaban kasar Faransa François Hollande REUTERS/Agency Pool
Talla

Jakadan Faransa a Najeriya Denys Gauer ya ce kasar sa ba za ta hada kai da wani bangare da ke neman balewa daga Najeriya ba, domin suna goyan bayan kasar kuma suna aiki tare.

Faransa wadda ta taimakawa Biafra a yakin basasar da aka yi a shekarar 1967 t ace anyi dare, kuma gari ya waye, saboda haka babu ruwan su ko kuma alaka da masu fafutukar kafa kasar Biafra.

Masu neman balewar daga Najeriya domin kafa Kasar Biafra na fafutukar samun goyon baya daga kasashen ketare wanda bai samu ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI