Masar

Kotu ta sanar da sallamar tsohon shugaban Masar

Hosni Mubarak tsohon shugaban kasar Masar
Hosni Mubarak tsohon shugaban kasar Masar REUTERS/Stringer/Files

A yau litinin mai shigar da karar a kasar Masar ya bada umarnin sallamar tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak, da a farkon wanna wata na maris kotun karya hukumcin ta wanke daga tuhume tuhumen kashe masu zanga zanga 2011. 

Talla

Lauya Farid el-Deeb ya tabbatar da cewa yanzu haka tsohon Shugaban kasar ta Masar Moubarak, da ake tsare a wani asibitin soja dake birnin Cairo na iya tafiya gida da zarar likitoci sun sallameshi

Hosni Moubarak, dan shekaru 87 a duniya ya yi mafi yawan zamansa kurkukun ne a asibitin sojan, da ke karkashin tsauraran matakan tsaro tun lokacin da aka kama shi a 2011.

A watan yunin shekarar 2012 ne aka zartar wa Mubarak hukumcin daurin rai da rai a gidan yari, amma kuma kotu ta sake bada umurnin yi masa wata sabuwar shara’ar .

A watan novemba shekarar 2014, kotun ta bada umarnin yin watsi da duk tuhume tuhumen da ake yiwa tsohon shugaban da ya mulki Masar sama da shekaru 30, zarge zargen da suka hada da kisa da kuma halata kudaden haram.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.