Nijar-Turai

Majalisar Dinkin Duniya ta damu dangane da bakin haure a Agadez

Yan cin rani kan hanyar zuwa Turai
Yan cin rani kan hanyar zuwa Turai REUTERS/Akintunde Akinleye

Shugaban hukumar kula da bakin haure ta Majalisar Dimkin Duniya OIM Williams Lacy Swing na ziyarar aiki a Agadez da ke Jamhuriyar Nijar, domin ganawa da hukumomi da kuma dimbin baki da ke kan hanyarsu ta ficewa zuwa arewacin Afirka da kuma Turai.

Talla

Agadez dai na a matsayin babbar matattara ga ‘yan asalin kasashen Afirka Kudu da Sahara ke amfani da ita a yunkurinsu na zuwa ci rani, to sai dai hukumomin kasar ta Nijar na iya kokarinsu domin shawo kan bakin wadanda ke jefa rayukansu a cikin hatsari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.