Somalia

Sojojin Somalia na zanga zanga kan albashi

Sojoji na zanga-zanga kan albashi a Somalia
Sojoji na zanga-zanga kan albashi a Somalia REUTERS/Feisal Omar

Daruruwan Sojojin Somalia sun gudanar da zanga zanga a birnin Mogadishu, inda suka tare hanyoyin ababan hawa da tilasta rufe shaguna saboda abinda suka kira rashin biyan su albashi.

Talla

Rahotanni sun ce an ga wasu sojojin dauke da makamai suna tare motocin da ke wucewa, yayin da wasu kuma suka bukaci masu shaguna su rufe su.

Captain Ali Osman ya ce sojojin suna tunawa sabon shugaban kasar alkawarin da ya yi cewar idan ya samu nasara zai biya su albashin su.

Wani hafsan sojin da ake kira Mohammed ya ce akalla sojoji 2,000 suka shiga zanga zangar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.