Wasanni

Wasan zari-ruga na fuskantar kalubale a Najeriya

Sauti 10:00
'Yan wasan kungiyar zari-ruga ta jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya
'Yan wasan kungiyar zari-ruga ta jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya nickandjaysadventures

Shirin duniyar wasanni na wannan makon ya tattauna ne game da kalubalen da wasan zari-ruga ke fuskanta a Najeriya, duk kuwa da irin namijin kokarin da 'yan wasan kasar ke yi a kasashen ketare. Abdurrahman Gambo Ahmad ya ziyarci filin wasan zari-ruga na jihar Kaduna, in da ya tattauna da 'yan wasan da suka bayyana masa irin nasarorin da suke samu a kasashen waje, amma gwamnatin kasarsu ba ta nuna halin-ko-in-kula ba, abin da suka ce yana rage musu kwarin gwiwa wajen ci gaba da kara kaimi.