Nijar
An yankewa Hama Amadou hukuncin daurin shekara guda a gidan maza
Wallafawa ranar:
Kotu a Jamhuriyar Nijar ta yanke hukuncin dauri na shekara guda a kan tsohon shugaban Majalisar dokokin kasar Hama Amadou wanda bayan da aka same shi da laifin sayo jarirai biyu daga Najeriya.
Talla
Da farko masu shigar da kara sun bukaci a yanke wa Hama Amadou hukuncin daurin shekaru 3 tare da hana shi rike mukamin siyasa har na tsawon shekaru 5 har aka same shi da laifi.
To sai dai lauyoyin da ke kare shi sun fice daga zauren shara’ar saboda a cewarsu an kauce wa ka’ida. To sai dai magoya bayan Hama Amadou na kalon hukunci a matsayin siyasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu