CAF

Najeriya ta bukaci NFF ta zabi Hayatou

Issa Hayatou ya shafe shekaru 29 yana shugabancin CAF
Issa Hayatou ya shafe shekaru 29 yana shugabancin CAF © RFI/Pierre René-Worms

Gwamnatin Najeriya ta bukaci shugabannin hukumar kwallon kafar kasar su marawa shugaban kwallon kafar Afrika CAF Issa Hayatou baya a zabensa da ya ke neman tazarce.

Talla

Wannan na zuwa bayan shugaban kwallon Najeriya Amaju Pinnick ya fito ya sanar da marawa Ahmad Ahmad na Madagascar baya wanda ke hammaya da Hayatou.

A ranar Alhamis ne CAF za ta zabi sabon shugaba inda Hayatou ke neman wa’adi na 8.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osibanjo ya umurci Pinnick ya zabi Hayatou saboda huldar da ke tsakanin Najeriya da Kamaru.

A cewar majiyar, gwamnatin Najeirya ta ce wajibi ne a zabi Hayatou ko da babu wata kasa da ke mara ma shi baya.

Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da wata hulda da Madagascar, don haka babu dalilin marawa dan kasar baya a zaben shugabancin CAF.

Masharhanta dai na ganin babu ruwan harakar kwallon kafa da siyasa, amma gwamnatin Najeriya ta ce ko baya ga makwabtaka tsakaninta da Kamaru da kuma yakin da suke da Boko Haram Issa Hayatou dan gida ne.

Shekaru kusan 30 Issa Hayatou na jagorantar hukumar kwalon kafar Afrika, tun a shekarar 1988.

Yanzu kuma Hukumar CAF ta takaita wa’adin shekarun shugabanta zuwa shekaru 12.

Tsarin shugabancin hukumar zai kasance na shekaru 4 a wa’adin shugabanci uku, kuma tsarin zai soma aiki ne daga zaben bana da za a gudanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI