Najeriya

Kwastam sun dakatar binciken takardun motoci a Najeriya

Hamid Ali, shugaban hukumar kwastam a Najeriya
Hamid Ali, shugaban hukumar kwastam a Najeriya

Hukumar Kwastam a Najeriya ta dakatar da shirinta na bincinke domin gano motocin da ba su da cikakkun takardun fito a cikin kasar.

Talla

Sanarwar da mai magana da yawun hukumar ta Kwastam Joseph Attach ya fitar a wannan laraba, ta ce an dage matakin ne bayan wata ganawa da aka yi tsakanin shugaban hukumar da kuma shugabannin Majalisun Najeriya kan wannan batu.

A marecen jiya talata, shugaban hukumar Kwastam Hamid Ali ya gana da shugaban Majalisar dattawan Abubakar Bukola Saraki, kwana daya kafin ya gurfana a gaban majalisar kamar yadda aka bukace shi ya yi domin kare wannan mataki.

Da farko dai hukumar ta Kwastam ta bai wa masu motoci wa’adin wata daya domin su tabbatar da cewa sun biya wa motocin kudin fito ko kuma su hadu da fushin hukumar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.