Nijar

An kama sama da CFA bilyan biyu na jabu a Nijar

Tsabar kudaden jabu da aka kama a Yamai Jamhuriyar Nijar
Tsabar kudaden jabu da aka kama a Yamai Jamhuriyar Nijar Actu

‘Yan sanda a Jamhuriyar Nijar sun cafke wasu mutane da suka shahra wajen sarrafa kudaden jabu tare da gabatar da su a gaban manema labarai a birnin Yamai.

Talla

Bayan kama wadannan mutane, an gano tsabar kudaden jabu sama da CFA bilyan biyu tare da wasu makudden kudade na kasashen ketare.

Wannan dai shi ne kame mafi muhimmanci da jami’an tsaron suka yi a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan a kokarinsu na fada da masu sarrafa kudaden jabu da kuma wadanda ke mu’amala da su a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.