Kamaru

Kamaru ta ceto mutane dubu 5 daga Boko Haram

Rundunar sojin Kamaru
Rundunar sojin Kamaru AFP PHOTO / REINNIER KAZE

Gwamnatin Kamaru ta ce, dakarunta sun yi nasarar ceto mutane dubu 5 da suka hada da mata da kananan yara da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su.

Talla

A cikin wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya gani, mai magana da yawun gwamnatin Kamaru Issa Tchiroma Bakary, ya bayyana cewa, dakarun sun kai samamen ne kan iyakokin kasar da Najeriya daga ranar 27 ga watan Fabairun da ya gabata zuwa ranar 7 ga wannan wata na Maris.

Bakary ya ce, samamen ya yi sanadiyar ceto mutane fiye da dubu 5 da Boko Haram ta yi garkuwa da su, da suka hada da kananan yara da mata da kuma tsofaffi.

Tuni dai aka kai mutanen sansanin ‘yan gudun hijira da ke Banki a Najeriya kamar yadda Bakary ya tabbatar.

Kimanin mayakan na Boko Haram 60 ne aka kashe a samamen, yayin da aka cafke 21 daga cikinsu kamar yadda Bakary ya yi karin bayani.

Duk da dai mahaifarta na Najeriya, kungiyar ta Boko Haram ta kaddamar da jerin hare-hare a kasashe makwabta da suka hada da Nijar da Kamaru da Chadi, abin da ya tirsasa wa kasashen kafa rundunar hadaka don yaki da kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.