Najeriya

Kotu a Najeriya ta bukaci a tsare Andrew Yakubu na NNPC

Tsohon Shugaban  kamfanin NNPC Andrew Yakubu
Tsohon Shugaban kamfanin NNPC Andrew Yakubu

Alkalin kotu a birnin Abujan Najeriya ya bayar da umurnin tsare tsohon shugaban kamfanin mai na kasar NNPC Andrew Yakubu wanda hukumar yaki da rasahwa EFCC ke zargi da aikata laifufuka shida masu alaka da rashawa.

Talla

A yau alhamis an gabatar da Yakubu a gaban kotu inda alkali ya bukaci a tsare shi har zuwa ranar 21 ga wannan wata domin duba bukatar ba shi beli, bayan da ya amince da cewa dala milyan 9 da dubu 800 da aka gano jibge a gidansa da ke Kaduna mallakinsa ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.