Najeriya

Yan Majalisu sun dage sauraran Shugaban Kwastam na kasa

Hamid Ali, shugaban hukumar kwastam a Najeriya
Hamid Ali, shugaban hukumar kwastam a Najeriya

Majalisar Dattawan Najeriya ta umurcin shugaban hukumar kwastam a kasar Hamid Ali mai ritaya da ya sake gurfana a gabanta a ranar laraba ta makon sama amma sanye da kakinsa na aiki, bayan da a yau alhamis ya je majalisar a cikin kaftani.

Talla

An dai jima ana kai ruwa rana tsakanin majalisar da kuma shugaban hukumar ta kwastam wanda ake son ya gurfana domin yiwa ‘yan majalisar karin bayani dangane da sabon shirin biyan kudaden fito ga motocin da aka shiga da su kasar.

Sai dai Hukumar Kwastam a Najeriya ta dakatar da shirinta na bincinke domin gano motocin da ba su da cikakkun takardun fito a cikin kasar.

Sanarwar da mai magana da yawun hukumar ta Kwastam Joseph Attach ya fitar a wannan laraba, ta ce an dage matakin ne bayan wata ganawa da aka yi tsakanin shugaban hukumar da kuma shugabannin Majalisun Najeriya kan wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.