Najeriya

Jirgin Aero ya datse yawan ma’aikatansa a Najeriya

Aero Contractors na cikin manyan jiragen Najeriya
Aero Contractors na cikin manyan jiragen Najeriya aero

Kamfanin Aero da ke jigila a Najeriya ya ce zai datse kashi biyu cikin uku na yawan ma’aikatansa a wani mataki na rage yawan kudaden da ya ke kashewa domin kaucewa fadawa ikon kulawar gwamnati.

Talla

Rahotanni sun ce sama da ma’aikata 1,000 Aero zai datse daga yawan ma’aikatansa 1,500.

Aero ya koma karkashin kulawar hukumar da ke kula da kadarorin gwamnati AMCON a Najeriya saboda dimbin bashin da ake binsa da kuma karancin jirage.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar AMCON Jude Mwauzor ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa Aero ba ya da kudaden da zai iya biyan ma’aikatansa albashi.

Aero da ke da jirage hudu yanzu ya koma yana jigila da jirage biyu yayin da ake kula da aikin gyran sauran jiragensa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.