'Yan bindiga sun kai wa 'yan agaji hari a Sudan ta Kudu
Wallafawa ranar:
Wasu 'yan bindiga a Sudan ta kudu sun kai hari kan wata tawagar kungiyar agaji, in da suka kashe mutane biyu daga cikin tawagar yayin da kuma suka jikkata 3.
Kungiyar kula da kaurar baki ta sanar cewar, 'yan bindigan sun kai harin ne kan tawagar da ke komawa daga garin Yirol, bayan sun ta yi musu kwanton-bauna, ta hanyar bude wuta.
Kungiyar ta ce ba ta iya gano maharan ba a kasar da ke ci gaba da fuskantar bala’in yunwa da yaki.
Ita ma kungiyar Medicins San Frotiers ta ce an kai hari a asibitin da take aiki a Wau Shilluk, in da aka kwashe magungunan da ke ciki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu