Ghana

Dole ne a nada ministoci 110 a Ghana-Akuffo-Addo

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo a yayin bikin rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasar bayan ya doke John Mahama a zaben da aka gudanar
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo a yayin bikin rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasar bayan ya doke John Mahama a zaben da aka gudanar REUTERS/Luc Gnago

Shugaban Ghana Nana Aufo-Addo ya kare matakin da ya dauka na nada ministoci 110 don tafiyar da gwamnatin karamar kasar da ke Yammacin Afrika. 

Talla

Matakin dai na ci gaba da shan suka daga al’ummar kasar musamman a shafukan sada zumunta.

Sai dai a wata hira da ya yi da gidan Talabijin na kasar, shugaba Akuffo-Addo ya ce, dole ne daukan irin wannan mataki don gaggauta samar da sauyi a Ghana.

Mr. Ado ya kuma jaddada cewa, sabuwar gwamnatinsa ba za ta bannatar da kudi ba kamar yadda Jama’a ke zato.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.